shara baji ba gani.
Bayan Malam Buhari ya fita ajin ya kaure da surutu.
Hauwa ta ce "gaskiya wasu Malaman suma akwai mugunta, ki duba ki gani tun d'azo suke sharar wajan can fa da alama wallahi sun jigatu"
"Uhmmm ai daga yanzu idan Malam Buhari ya shigo kinga sai kowacce ta kama kanta tayi shuru, ta rufa ma kanta asiri ai, tunda yanzu ansan halinsa ya tsani yana aji kana ma y'ar uwarka magana, kana masa surutun banza"
Hauwa zatai magana kenan suka ji ajin yayi wani shuru kamar mutuwa ta gifta da wajan.
Da sauri Atu da Hauwa suka kai dubansu a gaban Allo.
Ganin y'an SS3 ne suka cika ajin sunkai su biyar Maza biyu mata biyu.
A hankali wata daga cikinsu ta ce
"Surutun uban mi kuke mana?, kun cika mana kunne da surutu"
Shuru akai bamai iya bata amsa.
D'ayar ta sake cewa
"Ina shugabar class d'in nan take"
D'aya daga cikin y'an ajin ta ce
"Babu ba'a nad'a ba"
Wani namiji daga cikinsu ya nuna wata Binta dake zaune a gaba ya ce
"Kee daga yau ke ce shugabar ajin nan, daga yau idan muka zo muka taradda ajin nan ana surutu tofa kin shiga uku domin ko wanne hukunci a kanki zamu d'auka, dan haka da mun fita ki rubuta mana duk wacce tayi surutu a takarda, kin gane?"
Binta jikinta na kyarma badan tana son wannan shugabancin da aka bata ba ta amsa da eh.
Suna ficewa daga class d'in Binta ta zauna tana fashewa da kuka.
K'awarta Fiddausi ta dafata ta ce
"Kiyi hakuri yanzu dai ki yago faida ki fara rubutu duk wadda yayi surutu karma ki jama kanki".
Hauwa zata mik'e domin zuwa inda su Binta suke Atu ta rik'e mata hannu tana cewa
"Kee Hauwa mi kuma zakiyo wajansu?"
"Kinga ki cika ni na je na amshi faifar ni na rubuta mata, tunda naga ita da alama bazata iya ba"
"A'a fa Hauwa irin haka fa ne yasa na ce mu dawo baya da zama, da yanzu muna gaban da k'ila ni ce ko ke ce za'a nuna a matsayin shugabar class d'in nan, haka kawaii a d'ora maka nauyin da bazaka iya dashi ba, duk irin haka nake gudu"
Badan Hauwa taso ba ta koma ta zauna, tana hararar Atu tana mitar tana shigar mata hanci a kudundine wallahi.
Atu ta ce "eh na dai ji komi zaki ce, ki ce dai saura kije kiyi abun ya k'are kanmu, dama sai tsaya iya ke kad'ai ne to"
Su Binta suna d'akko Faifa ta mik'e a tana cewa
"To wallahi yanzu zan fara rubuta masu surutu duk wadda ya bari sunansa ya shiga a nan cikin faifar babu ruwana nayi gargad'i karma ka ce na fara ban sanar ba"
Tana gama fad'ar haka ajin yayi shuru, sai marassa jin ajin wasu dake magana k'asa-k'asa suna rad'a duk tana kallon kowa tana halkance da kowa, duk wadda ta ci karo da bakinsa na motsi rubutasa take kawai........
*RAYUWAR MAKARANTA*
*©Zahra Royal Star*
Page 2
A hankali aka buga k'araurawar fita break, gaba d'aya ajin ne ya d'auki surutu kowa ya d'auki y'ar jakar sa had'e da kular abincin sa yayi waje.
Hauwa ta kalli y'an bayansu dana gabansu ta ce
"Sorry amma ya sunanku ne?"
Harara Atu ta makama Hauwa tana k'ok'arin janta su fice waje amma ta dake tana kallon wa'inda ta tabbaya.
Murmushi suka saki, d'aya daga cikinsu ta ce
"Ni sunana Hadiza, wannan kuma Ammama sai kuma Fatee"
"Masha Allah, ko zamu iya zama K'awaye"
"Eh man babu damuwa ai, kuzo mu fita waje, inda muke zama muci abinci, naga kamar yau kuka fara zuwa ku hakane?"
Murmushi Hauwa ta saki tana cewa
"Eh yau muka fara zuwa"
Ficewa sukai a tare suna raha kamar sun dad'e da sanin juna, ba abunda Atu keyi sai kunbure-kunbure danmi Hauwa zata jawo masu wasu a cikinsu.
Zama sukai akan wasu duwatsu su duka. Atu na kallon yanayin makarantar kota ina d'alibai ke wucewa wasu na tafiya gida break, suna bi ta cikin daji su wuce. School d'in akwai girma sosai ta yadda zaka iya fita ta bayanta ta cikin jeji, ka dawo kowa bai sani ba, shi yasa da Malamai suka gane har nan wajan ana zuwa taran makara, saboda wasu y'an iskan school d'in suna biyowa ta cikin daji da safe.
Maganar Hauwa ta katse d'an shurun daya gifta jin tana cewa
"Wow Hadiza kwad'on tuwo kikazo dashi?, kai wallahi ina son kwad'on daddawa kuwa"
Murmushi Hadiza tayi tana kallonta tana yayyaka tuwon data zo dashi tana niyar kwad'awa ta ce
"Eh da shi nake zuwa, ku ai naga y'an gayu ne ku, da indomi da kawai fa kuka zo dashi"
Hauwa ta tab'e baki cike da jin haushin abunda ya faru d'azo bayan fitar su aji, kamin su shigo class sun aje kayansu sadda zasu dawo an bud'e kular su an sace Kwan guda biyu ba'abar ko guda ba, anci rabin indomin anbar masu sauran.
Tab'a ta Fatee tayi tana cewa
"Hauwa ga kwad'on mai da yaji ni kuma na Yi, Bismillah. Tunanin mi kike naga kinyi shuru?"
Tsaki Hauwa tayi tana cewa
"Wallahi abinci muka bari a cikin aji d'azo da safe muka tafi house d'inmu domin yin aiki da shara, sadda za'a shigo aji an samu wani d'an iskan ya bud'a mana abinci ya cinye rabi"
Dariya Ammama ta saki tana cewa
"Kashh dan yau ne zuwanku na farko shi yasa, amma ai wake barin kayansa a cikin aji ya tafi yawo, ai in gaya maku ba'a yin haka nan, daga yanzu ko jakarku karku sake ku k'ara barinta a class idan zaku fita, ku rink'a sagala abunku ku fita da ita"
Atu data fara cin indominta ta kalli Ammama bakinta cike da abinci ta ce
"Tofa ashe class d'in namu akwai b'arayi tabd'i jam"
"Ai ko b'arayi ma idan kinji b'arayi, baka da damar aje abunka mai mahimmanci a class ka fita, baka dawo kaga anyi ciki dashi ba"
Cewar Hadiza ta idasa maganar tana kai kwad'on tuwo a bakinta bayan ta gama kwad'a shi.
Wani faranti ta d'akko ta zubama Hauwa ta mik'a mata.
Amsa tayi ta fara ci. Atu dake kusa ta ce
"Ni dai na k'oshi ga Indomi idan zaku ci, ke kuma Hauwa baki cin indomin ne?"
Hauwa ta cinye kwad'on data d'ebo zata kai bakinta bayan ta had'iye ta ce
"A'a ni bazanci ba gaskiya ki basu idan zasu ci to, amma ni abun ne ya fice min a rai tunda aka bud'a aka cinye rabi na ce dama wallahi bazanci ta ba"
Tab'e baki kawai Atu tayi tana juyowa gasu Ammama dake ta d'arkar abincinsu, zatai magana ta kalli Ammama, sake da baki ganin yadda ta wani cire hijab ta d'aureta a k'ugunta sai faman cin kwad'onta take babu abunda ya sha mata kai.
Atu ta kasa hakuri ta ce
"Ammama miye haka Kuma Fisbilillahi?"
Ammama bakinta cike da kwad'on tuwo bata had'esa ba ta ce
"Mi kuma nayi?"
Atu ta nuna ta da yatsa tana cewa
"Dube ki dan Allah kin wani yaye hijabinki kina cin abinci, kuma ga mutane Maza na wucewa ta wajan nan"
Dariya Ammama ta saki tana duban Atu ta ce
"Ke nifa haka nake cin abinci na, dan yau kuka fara zuwa shi yasa zaku yita ganin sabbin abubuwan da baku saba gani ba, ke dai ci abincinki kawai, ai wajan ba hayaniyar mutane ma, shi yasa muka zab'i zama bayan gidajan Malamai arna da ake kawowa daga wata uwa duniya"
Zaro ido Hauwa tayi tana amshe zancen da cewa
"Kee dan Allah wai a nan wajan wasu ke kwana Malamai?"
"Kware da gaske kin dai gani, a nan suke kwana"
Hadiza ta bata amsa
Hauwa ta gyara zamanta akan dutsin da take zaune ta d'an gaji da zama a samansa kad'an ta d'an yatsine baki tana cewa
"Tabd'i jam, basu gudun dare yayi, yanzu Fisbilillahi ai bazan iya zuwa koda hanyar school d'in nan ba ce cikin dare bare ace na shigo cikinta, duba ki gani miye zai hana Tanbotse a school d'in nan, kota ina daji ce fa, gabas Kudu yamma arewa ki duba fa"
Ta k'are maganar tana faman nuna yanayin school d'in da hannu.
Hadiza zatai magana aka buga k'araurawar komawa class.
Da mugun sauri Ammama ta fara had'a kayanta data babbaje a wajan.
Su duka tashi sukai suna saurin had'a kayansu.
Hauwa ta dube su da d'an mamaki tana cewa
"Kubi a hankali mana wannan sauri haka?"
Hadiza ta kalleta da mamaki, sai kuma tayi murmushi tana kauda mamakinta ta ce
"Har yanzu da sauranki Hauwa, yo ai nan idan ba saurin mukai ba aka rufe mintina ashirin ko goma yanzu nan zakiga y'an SS3 sun fara jifgar mutane, danmi baka koma class cikin lokaci ba, bugu suke nake gaya miki duk wadda aka gani a waje bare idan ba'a dad'e da komawa break ba, gara muje ajin mun idasa acan, bana son abunda zai tab'a lafiyar jikina"
Atu data yi gaba tunda taji abunda Hadiza ta ce domin tama fi Hadiza rashin son a tab'a lafiyar jikinta.
Da sauri suka take mata baya a haukace kamar sabbin mahaukata suka idasa class d'in, domin har sun fara bugun duk wa'inda sukai saura a waje, ko kuma asa mutum tsallan kwad'i har sai ya idasa class da tsallan kwad'in.
Suna shiga suka baje akan kujera da yake kujerarsu tana kusa da juna ce, a haka suka fara uban surutu suna yi suna idasa cinye abincin da yayi saura.
Suna cikin haka suka ji class ya d'au shuru, ba shiri har Ammama na niyar kifar da sauran kwad'onta dake akan cinyarta ta kusa cinyewa ta tashi tsaye.
Da sauri kuma ta koma ta zauna tana rufe kular da sauri ta sata a k'ark'ashin kujera.
Y'an SS3 ne wa'inda d'azo suka bada umarnin a rubuta masu, masu surutu.
Jikin kowa yayi sanyi sai binsu ake da kallo.
Wata daga cikinsu tana yatsine baki ta d'an dod'e hancinta tana cewa
"Ohhh My God, class sai warin daddawa yake, dubeku k'azamai da'aAllah"
Wata ta dafa mai maganar tana cewa itama
"Ke kam Salma ai dole suyi k'azanta baki ganin har yanzu yarintar primary bata idasa sakinsu bane, duk sun cikama mutane aji da warin daddawa"
Itama ta idasa fad'ar haka cike da isgilanci suna watsa masu wani mugun kallo.
Ba wadda ya isa yayi koda tari ne a cikin ajin suna dai kallonsu kawai.
D'aya daga cikin Mazan ne ya ce
"Ina shugabar class d'in take?"
Da sauri Binta ta mik'e tana cewa
"Gani nan"
"Yawwa ki fiddo da faifar da kika rubuta mana y'an surutu ki fito gaban allo ki kira sunan kowa, kowacce taji sunanta ta fito nan gaban allo"
Ya idasa maganar yana kallon y'an class, da yawansu tsoro ya cika masu zuciya kowa na addu'ar Allah yasa dai baiyi surutu ba, Allah yasa dai ba sunansa a ciki.
Wato sunan data fara kira ne ya ba y'an class mamaki ba kad'an ba, wato Hauwa Rabi'u.
Da mugun mamaki Hauwa ta mik'e tana kallon Binta kallo irin na zaki ci uwarki ne idan na kamaki wallahi.
Atu ma dai mamaki take, ta ina Hauwa tayi surutu?, domin ita ce ta hanata yinsa da ba abunda zai hanata tayi komai ta fanjama fanjam.
Da haka tayita kiran sunaye ta kira ya kai mutum goma Sha.
Ba tausayi ko tausayawa a tafin hannunka zata ware a nan suka rink'a bugun wa'inda sukai surutu, bulala goma-goma.
Tabbas bulalar ta shigi Hauwa ba kad'an ba, domin tafin hannunta sunyi jawur.
Bayan ta koma kujera tana ta kallon Binta tana ayyana miya kamata tayi ma yarinyar nan ne ma?.
Bayan sun fita harda bada umarnin a sake rubuta wasu y'an surutun.
Hauwa ta mik'e bata sauka a ko ina ba sai a gaban kujerar su Binta.
Gaban kujerar ta buga da hannunta tana kallonta ido cikin ido ta ce
"Keee dan Ubanki ubanmi nayi miki da har zaki saka sunana a cikin y'an surutu, al'halin kuma banyi surutun ba?"
Shuru Binta tayi tana faman murgud'a baki.
Hauwa ta ce "kan Ubancan"
Ta shak'o wuyan hijab d'in Binta, y'an class na kallo babu wadda yayi gigin shiga fad'an, kowa na kallo, wasu ma so suke suga anci uban Binta, bare wa'inda ta rubuta sunansu cikin y'an surutu.
Hauwa ta sake cewa
"Zaki gaya min uban mi na tsare miki, ko kuwa saina gurji bakin shegiya yanzun nan?"
Binta ganinfa idan ba dagewa tayi ba itama tofa zata bata kunya ne a gaban y'an class mutumcinta ya zube.
Itama taci kular hijab d'in Hauwa tana cewa
"Naje na saka kiyi duk abunda kika ga zaki iya, da bakiyi ba zan saki ne?"
"Kutumar uba kaii yau zanci uban wata a nan wajan wallahi, har yanzu ban nuna maku kala ta ba wallahi a cikin class d'in nan, dole na fito da kalata ko an zauna lafiya, domin naga idan ba haka nayi ba bazan zauna k'alau da kowa ba"
Hauwa na k'are maganar ta daddage iya k'arfin ta kaima Binta wani naushi a tsakiyar bakinta, ai ko nan take bakin ya fashe ya haye yayi suntum ba kyan gani.
Wata uwar kururuwa Binta ta saki tana kuka tana cewa
"Wayyo Allah na shiga uku na, ta fasa min baki, na rantse da Allah bazan yarda ba, idan na yarda Allah ya tsine min"
Hauwa data sake ta tana rik'e da k'ugunta tana wata girgiza ta tsallar neman fitina tana makama mata harara ta ce
"Ai ko yau sai dai Allah ya tsine miki yarinya, kuma wallahi na sake naji wata magana ta fito daga shegen bakin nan naki akaina saina miki abunda yafi wannan kin san hali na yanzu sarai ba sai na tsaya na sake miki wani dogon bayani ba, gobe ma dan Allah ki sake rubuta sunana a cikin y'an surutu kin ji?"
Kuka kawai Binta ke yi domin ta lura Hauwa idan ta biye mata tofa dukan banza zata ci, dan bata da k'arfin k'arawa da Hauwa. Dole tasa ta koma ta zauna y'an class sai faman mata dariya suke k'asa-k'asa wai danma suna tsoron kar su fito fili da dariyar taci uban shege wajan sa sunansa a cikin y'an surutun aji.
Ai ko kamar sun sani duk wadda taga bakinsa na murmushi ko alamar dariya sunansa kawai take dafkawa a cikin faifar dake gabanta.
Kuma sai akai sa'a babu malamin daya sake shigowa har Hauwa tayi ta'asarta ta koma ta zauna.
Ammama har saurin cewa take "kai amma wallahi kin birge ni, da kika yi ma shegiya haka, dama haushi take bani, sai wani iyayin tsiya cike da ciki, kinyi maganinta ai"
Atu ta harari Hauwa tana cewa itama
"Keee dai Hauwa kinji dad'i wallahi, ke dai idan baki nemi magana ba baki jin dad'i a rayuwarki"
Kallonta Hauwa tayi rai d'an b'ace ta ce
"Dakata Atu miye nayi na jan magana a nan wajan kuma?, ita duk abunda tayi min baki gani ba kenan?, sai ni kike ganin laifi na, saboda dama na saba haka ko?".
"Hmmm"
Kawai Atu ta ce tana gyara zamanta a cikin kujerar da suke tana fuskantar Hauwa kamin ta ce
"Ko kad'an ba haka bane, itama batai dai-dai ba, domin Allah d'azo banga ko naji kinyi surutu ba, amma ai bai kamata kiyi mata haka ba ko?"
D'aga mata hannu Hauwa tayi tana cewa.
"Kinga kefa na lura bak'i k'i na barta taci bulis ba, kuma kema kin san bazan tab'a bari ba, idan ba'a tab'a ni ba ai bazan tanka ba, dan haka ki kama bakin ki kiyi shuru kawai yafi miki"
"Ai shikenan ina gudar miki ranar da zaki tab'o wacce tafi ki iya rigima ranar ta gurji baki babu abunda zanyi kuma ba"
Hauwa zatai magana kenan Malam ya shigo class d'in, dole tasa tayi shuru suna mik'ewa gaba d'aya suna gaisar dashi.
Har ya fara goge allo da kansa sai kuma ya juyo inda su Binta suke yana cewa
"Ina shugabar class d'in nan ta zo ta goge min allon nan?"
Nuna masa Binta akai dake rik'e da bakinta har yanzu yana mata wani zugi, daurewa kawai take.
Kallonta yayi sosai yana cewa
"Ke mike faruwa ne da bakin naki?"
Da kyar ta bud'e bakin maganar ma da kyar take yinta ta ce.
"Malam bigewa nayi da bango ban lura ba, shine yasa ya kunbura haka"
Daga can baya Hauwa ta saki wani murmushin gefen baki, tana duban Atu data saki baki tana maganar zuci. Wato kenan dai Hauwa taci bulis, yarinyar nan ta fara tsoronta.
"Allah ya shirya ki Hauwa"
Atu ta fad'a a hankali yadda ita kad'ai zata ji ta.
Murmushi ta saki itama tana ce mata.
"Amin idan da gaske kike"
Hararar wasa Atu ta maka mata kawai tana girgiza kanta, suka maida hankalinsu ga Malamin da yake ba Binta amsar cewa.
"Ayyah sannu fa, sai a rink'a kula daga yanzu, kije wajan y'an SS3 ki tabbaya ina Health take za'a nuna miki ita ki ce ta baki magani, zata baki"
Girgiza kai tayi da sauri domin bata son abunda zai had'a ta da y'an SS3 ita a yanzu ta ce
"A'a Malam idan naje gida zansha kawai"
D'aga k'afad'arsa yayi yana d'an tab'e baki ya juya ya ci gaba da lasin nashi.............
*RAYUWAR MAKARANTA*
*©Zahra Royal Star*
Page 3
"Dan Allah ki tak'o k'afa mu wace dajin nan, kinsa an tashi school mun biyo ta cikin daji haba dan Allah, kuma kin k'i kiyo sauri"
Cewar Atu dake tafiya da sauri, domin dajin tsoro ma yake bata.
Hauwa dake kallon wasu dondozen y'an mata su uku dake biye da su suna tafiya suna nuna su kamar masu neman rigima dasu yasa Hauwa d'an tsayawa tana cewa
"Kee tsaya dan Allah kamar fa Binta nake gani tare da wasu, miye take nufi ne, badai jawo wasu tayi ba domin su rama mata abunda nayi mata ba?"
Da sauri Atu ta waiga tana d'ora hannunta a saman kanta ido a waje take cewa.
"Shikenan mun shiga uku, yanzu miye kika ja mana ne haka?, da munbi su Hadiza da duk haka bata faruwa ba, da yanzu na sani mun shiga cikin gari ma"
Tsaki Hauwa tayi tana rik'e k'ugunta tana sake kallon y'an matan da suka k'araso kusa dasu yanzu.
Binta dake kallon Hauwa ta makama mata harara tana nunata da yatsa ta ce
"Yawwa anti Amina ita ce ta bige min baki a cikin aji babu uwar dana yi mata Kuma"
Wani kukan kura Amina tayi sai gata a gaban Hauwa tana k'ok'arin shak'o wuyan hijab d'inta tana cewa
"Kutumar uban miye tayi miki da har zaki fasa mata baki?"
Da sauri Hauwa ta matsa gefe hakan yasa hannun Amina bai kai jikinta ba, ta dubeta a wulakanci babu tsoro akan fuskarta ta ce
"Kinga Malama karki sake k'azamin hannunki yayi gigin tab'a min jiki wallahi, kuma na fasa mata bakin ko akwai abunda zaki yi ne a akai?"
"Jar ubancan kayyasa, ke Amina kika tsaya wannan k'aramar al'hakin take gaya miki magana son ranta baki ci uwar shegiya ba"
Cewar wata dage gefe mai d'an jiki domin da kyar take tafiya ma tsabar y'ar kibar da taima jikin nata yawa.
Atu dake gefe ta matso cike da tsoro ta ce
"Kuyiwa girman Allah kuyi hakuri, bazata sake ba nan gaba in..... Da mugun sauri Hauwa ta katse Atu da cewa.
"Kaiii amma dai Allah ya isa tsakanina dake wallahi, miye ruwanki a cikin fad'an nan, wa'innan zan ba hakuri? Ubangiji ya kiyaye ni, dan haka kiyi min shuru da bakin nan naki"
Hauwa na rufe bakinta Amina ta ribaceta ta duk'a ta kamo k'afarta kawai sai dai Hauwa taji anyi zama da ita an fyad'a da k'asa.
Ihu Hauwa ta saki tana sakin wata uwar kururuwa mai k'arar gaske, juye-juye ta farayi tana birgima a k'asa kamar macijiya, tana yi tana wasu surutai kamar wacce aljanu suka shafa.
Zaro ido su Amina sukai suna duban Binta cike da tsoro Amina ta koma gefe tana cewa.
"Mun shiga uku ke Binta ba dai mai aljanu kika kwaso mana ba, kinfa san ina tsoron mai aljanu?"
Binta da y'an cikinta ke kuka itama ta ce.
"Wallahi ban sani ba, yaufa suka fara zuwa makarantar"
"Shegiya amma shine kika bari muka haye masu da rigima haka kawai, baki gama fahimtar wace ita ba, ki ja mana masifa"
Cewar mai k'ibar cikinsu sai zufa take sharcewa ganin yadda Hauwa ke wata irin lankwasa kamar macijiyar gaske.
Atu dake gefe itama bala'in tsoro ne ya rufe ta duk d'aukarta ko aljanun gaske ne suka shigi Hauwar a yanzu.
Basuyi aune ba Hauwa ta mik'e ta rarumo Amina ta kad'a da k'asa ta haye ruwan cikinta ta fara kai mata yakushi a fuskarta kota ina.
Ihu Amina take tana k'arawa tana cewa.
"Wayyo Allah na shiga uku nah dan girman Allah kuyi hakuri na rantse banzan sake shiga harkar god'iyarku ba, ku yafe min dan Allah"
"Wuuyihohooo sai ni d'an gidan sarkin aljanu, ubanwa yasa ku tab'a min masoyiya Abar k'auna ta, yau sai kun gano duniyar aljanu yau sai kun d'and'a kud'arku wallahi"
Cewar Hauwa tana yi tana ihu had'e da lauyar da harshe kamar mai aljanun gaske, idan kaga yadda take baka tab'a cewa ba aljanun gasken bane.
Mai k'ibar nan ce ta daddage iya k'arfin ta banga je Binta dake nanik'e da ita ta zura da uban gudu ko waige bata yi, tana cikin gudu wani dutse ya tab'e ta, ta zube a k'asa rikijahh, ihu ta saki tana tashi da kyar duk ta ji ciwo a hannunta da gwaiwarta amma tsabar tsoro haka ta mik'e ta ci gaba da tik'a gudu kamar wacce mutuwa ta biyo.
Duk da irin halin tsoron da Atu take ciki hakan baisa ta kasa dariya ba, tana kallonta yadda take gudu da kyar.
Sai da Hauwa ta tabbatar Amina ta bugu iya buguwa sai kawai ta sauka kanta tana faman sakin tashiwa. Haba kamar jira take tana ganin ta sauka akanta, Amina ta mik'e duk da irin dukan data sha, ta fanska da gudu itama, ganin haka Binta ta take masu baya.
Hauwa na ganin sunbar wajan ta mik'e tana kakkab'e jikinta tana sakin wata uwar dariya har tana d'aukewa k'asa harda su kwanciya tsabar dariyar mugunta.
Kallonta Atu take cike da mamaki tana cewa.
"Wai tsaya ba dai aljanun k'arya kikai masu ba?"
"Ke duk zama da nake tare da ke na tab'a tayar da aljanu ne?, ai kema kin san banda wasu aljanu"
"To amma ke dai kam baki da mutumci wallahi, kinga Hauwa ki kiyaye kanki da k'arya irin wannan, sai na gasken sun shiga jikinki haka kawaii su shiga jikinki a banza, sufa ba'a masu haka wallahi in fad'a miki"
Da sauri Hauwa ta mik'e ta fara tafiya Atu ta take mata baya tana cewa.
"Kefa matsalata dake yima mutum mugun fata wallahi, yanzu miye nayi wadda ba dai-dai ba iyee?, baki ga mutanan data d'ebo min bane, idan na ce zan tsaya tofa jifgata zasuyi la'ada waje wallahi ai sarkin tawa yafi sarkin k'arfi, yanzu wannan rusheshiyar dana gani tare dasu idan ta haye ruwan cikina ai na shiga uku na, amma yanzu dana yi masu haka baki ga yadda suke gudu ba kamar wa'inda mutuwa tayi ma sallama"
Atu ta sauk'e ajiyar zuciya tana cewa.
"Tsakani da Allah Hauwa kinfi k'arfin kaina, kowaye ya shigo komarki ya bani ya shiga uku wallahi"
"Yo a'ato kinga laifi na ne?, idan ba haka kayi ba naga alamar bazaka zauna da kowa lafiya ba, yanzu da irin hakurin da kike badawa nayi masu ai da yanzu wata maganar ake ba wannan ba yarinya, gobe ma su sake shiga harkata, ke basu bama wallahi hatta y'an SS3 ko Malamai suka ce zasu k'ara min muguntar da bata gimshe ni ba mataki kawai zan d'auka da bazai masu dad'i ba".
Atu da d'an daka ta da tafiya tana cewa.
"Kinga Hauwa ina jiye miki ranar nadama, kinga ki rufa ma kanki asiri abun naki ya tsaya iya d'alibai kad'ai banda Malamai, D'aliban ma banda y'an SS3"
Wani uban tsaki Hauwa ta saki tana hararar Atu ta ce.
"Kefa baki da wayo wani lokacin, babu abunda zan fasa wallahi, su y'an SS3 uban waye su da baza masu hakan ba, mi yasa suke jifgar yaran mutane, so kawai nake su k'ara shiga gonata wallahi".
Har suka isa inda zasu rabu ko wacce ta wuce gidansu Atu bata k'ara magana ba, sai da Hauwa zata wuce ta santar gidansu taji Atu na cewa.
"Dan Allah gobe ki fito da wuri, dan wallahi bazan sake bari na makara ba, kisa nayi tsallan kwad'i ko wankin toilet, kin san dai bazan bari a dake ni ba, ki rufan asiri ki fito da wuri"
Da to kawai Hauwa ta amsa tayi gaba abunta.
Tana gaf shiga gidansu taji wani yaro ya kwashe da dariya yana kallonta.
Da mugun sauri ta kai dubanta gare sa a d'an mamakance take dubansa tana nuna kanta ta ce.
"Kai da ubanwa kike?"
Dariya yaron yayi yana nunata yana cewa.
"Wai kin ganki kuwa kamar wacce tayi birkid'a cikin k'asa wahoho ku dubeta kamar wata biranya"
Yara suka taro